Home Labarai Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 9 kan hanyar Kaduna-Abuja

Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 9 kan hanyar Kaduna-Abuja

75
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 9 kan titin Abuja-Kaduna bayan sun yi musayar wuta.

A cikin wata sanarwa daga Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, ta ce sojojin sun hallaka ‘yan ta’addar ne a lokacin da suke kokarin tsallaka titi.

A cikin sanarwar, gwamna Nasir El-Rufa’i ya yi roko ga daukacin jama’a da a kodayaushe su rika sanar da duk wani yunkurin kai hari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply