Home Labarai Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram da dama a Gubio

Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram da dama a Gubio

148
0

Rundunar Operation Lafiya Dole, ta kashe ‘yan Boko Haram da dama, wadanda suka yi yinkurin kai hari a garin Gubio da ke jihar Borno.

Shugaban sashen yada labaran rundunar tsaron Manjo Janar John Enenche ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Enenche, ya ce hadin gwiwar sojojin sama ne da na kasa, suka kai harin da ya murkushe ‘yan ta’addan.

A cewar sa, jirgin ya hango ‘yan ta’addan a cikin motocinsu na yaki, nan take ya yi nuni da jirgin yakin ya kaddamar masu, wanda hakan ya yi sanadiyyar tarwatsa motocin yakin ‘yan Boko Haram, dama wadada ke cikin su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply