Home Labarai Sojoji sun murkushe ‘yan bindiga a Sokoto da Zamfara

Sojoji sun murkushe ‘yan bindiga a Sokoto da Zamfara

163
0

Shelkwatar tsaron Nijeriya ta ce rundunar Operation Hadarin Daji, ta yi nasarar tarwatsa gungun ‘yan bindiga a wasu hare-haren kakkabe ‘yan bindigar da suke kaiwa a jihohin Sokoto da Zamfara.

A wata sanarwa da Jami’in yada labaran rundunar Manjo Janar John Enenche ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, ya ce wannan aiki na daga nauyin da aka dorawa rundunar, na kakkabe ‘yan bindigar daga yankin Arewa maso yammacin kasar.

Enenche ya ce a ranar 11 ga watan Yuli, dakarun suka yi arangama da ‘yan bindigar, wanda suka saci shanun da ba a tantance yawan su ba, a Daki Takwas da Tashar Kuturu da ke kananan hukumomin Anka da Talatar Mafara a jihar Zamfara, wanda hakan ya yi silar mutuwar ‘yan bindiga da dama, wasu kuma suka gudu da harbin bindiga a jikin su.

Ya ce an kwato shanu 302 da tumaki 412 daga hannun ‘yan bindigar da kuma wayoyin hannu biyar da bindiga kirar jigida, yana mai cewa tuni aka mayar da shanun ga masu su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply