Dakarun haɗin gwiwar rundunar Operation FANSAN YAMMA sun halaka ’yan ta’adda biyu tare da cafke wani da ake zargi da safarar ababen fashewa guda 180 a jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dakarun sun gudanar da ayyukan ne a ranar Juma’a, yayin da suke ƙara tsaurara hare-hare kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda da hanyoyin da suke amfani da su wajen samar da makamai da kayan aiki.
A yayin wani samame da runduna ta 2 ta gudanar a yankin Garin Kaso da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji, dakarun sun yi arangama da ’yan ta’adda, lamarin da ya haifar da musayar wuta.
A sakamakon arangamar, an halaka ’yan ta’adda biyu, yayin da dakarun suka kwato bindigogi biyu, magazin guda biyu, harsasai tara da babura biyu.
Bayan haka, wasu ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin yi wa dakarun kwanton bauna daga wuraren da suka ɓuya, amma sojojin sun fatattake su tare da jikkata wasu daga cikinsu.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar JTF North West, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ba a kai ga tantance adadin waɗanda aka kashe ko jikkata a arangamar ta biyu ba.
Ya ce rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa wasu ’yan ta’addan da suka tsira sunga gawarwakin mutanen tare da wasu da suka samu raunukan harbin bindiga.
A wani samame na daban a wannan rana, dakarun sun cafke wani mutum mai shekaru 57 mai suna Sani Umar, wanda ake zargi da safarar makamai da abubuwan fashewa.
Binciken motarsa ya kai ga gano ababen fashewa 180 na nau’in 20mm Super Power, waɗanda ake zargin yana jigilar su daga ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara zuwa ga wasu ’yan ta’adda da ke aiki a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
An kama wanda ake zargin tare da motarsa da kuma kayan da aka gano, inda aka miƙa su domin ci gaba da bincike.
Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin ƙoƙarin da take yi na kai hari kan maboyar ’yan ta’adda tare da katse hanyoyin da suke samun makamai, abubuwan fashewa da sauran kayan aikin aikata laifuka.
