Home Labarai Sojojin Nijeriya ba su son yaki da ta’addanci ya kare – Dr....

Sojojin Nijeriya ba su son yaki da ta’addanci ya kare – Dr. Gumi

26
0

Sanannen malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya yi zargin cewa sojojin Nijeriya ba su so a kwaranye matsalar tsaron kasar nan, saboda su na amfana da lamarin da ake ciki, acewar jaridar Daily Nigerian.

Dr Gumi ya yi wannan zargin ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise, kwanaki kadan bayan kammala ziyarar tattaunawa da ‘yan ta’adda a arewacin kasar.

DCL Hausa ta samu labarin cewa Dr Gumi yace ganawarsa da ‘yan ta’addar ta sanya ya gano wasu bukatunsu da ke da bukatar a cika musu, wanda yace muddin aka cika musu, harkar ta’addanci za ta zamo tarihi.

Ya yi takaicin cewa sojoji ba su ba da hadin kai, inda ya yi zargin cewa mafiyawa suna ba da gudunmuwa wajen ruruta wutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply