Home Sabon Labari Sojojin Nijeriya ba za su iya yaƙi da ƴan bindiga ba –...

Sojojin Nijeriya ba za su iya yaƙi da ƴan bindiga ba – Sen. Gobir

264
0

Sanata mai wakiltar Sokoto ta Gabas a majalisar dattawan Nijeriya Ibrahim Gobir (APC) ya ce sojojin Nijeriya sun nuna gazawa wajen yaƙi da ƴan bindiga a yankin.

Gobir ya bayyana haka ne a zaman majalisar na ranar Talata, lokacin ƙin nuna amincewa da ƙudirin da mataimakin mai tsawatarwa na majalisar Sabi Abdullahi ya gabatar kan umarnin shugaba Buhari ga sojoji, su kawar da ƴan bindiga daga wasu jihohi.

Sanatan ya ce jama’ar yankin sun gwammacewa neman ɗauki daga sojojin Nijar a duk lokacin da aka kawo masu hari, maimakon na Nijeriya.

Majalisar dai ta yaba da matakin na Buhari kan umarnin da yaba sojoji su kawar da ƴan bindigar a jihar Katsina.

Sannan kuma sun buƙaci a faɗaɗa umarnin har zuwa jihohin Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto da dai sauran su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply