Home Labarai Sojojin “Operation Sahel Sanity sun kama ‘yan bindiga 38 da alburusai 941

Sojojin “Operation Sahel Sanity sun kama ‘yan bindiga 38 da alburusai 941

118
0

Rundunar tsaron soji mai lakabin “Operation Sahel Sanity” ta ce ta yi nasarar cafke ‘yan bindiga 38 daga 4 ga watan jiya na Satumba, zuwa 25 ga Oktoba, 2020 a arewa maso yammacin Nijeriya.

A taron manema labarai da rundunar ta musamman ta kira a matsuguninta da ke Faskari, jihar Katsina, ta ce ta kuma yi nasarar kama masu ba ‘yan ta’adda bayanan sirri su 93 a cikin wannan lokacin.

Mai kula da sashen watsa labaran rundunar Col. Ahmad Iliyasu ya ce “Operation Sahel Sanity” ta kuma yi nasarar ceto karin mutane 108 da aka yi garkuwa da su.

Col. Iliyasu ya ce sun kuma yi nasarar ceto shanu 131, awaki da tumaki 154 tare da tabbatar da hannanta su ga masu su na ainihi.

Ya ce sojojin sun kuma kama dillalan da ke cinikin shanun sata, tare da dakile hare-haren ‘yan bindiga har sau 47 a cikin wannan kankanin lokaci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply