Home Labarai Sojojin ruwa sun kama buhunan shinkafa 31,310

Sojojin ruwa sun kama buhunan shinkafa 31,310

45
0

Babban kwamandan rundunar sojin ruwa mai kula da shiyya Gabas Calabar David Adeniran yace sojojin ruwa sun lalata matatun mai 291 da aka gina ba bisa ka’ida ba.

Rundunar tace ta kuma yi nasarar kwace buhunan shinkafa 31,310 tare da kama wadanda ake zargi da aikata laifukan su 707.

Adeniran na fadin irin nasarorin da ya samu a lokacin da ya ke aiki kafin ya yi ritaya a ranar 4 ga watan Janairu, 2021 a birnin Calabar na Cross River.

Yace rundunar ta a zamanin mulkinsa, ta kwace tan-tan na danyen mai 1,000 sannan kuma ta kwace tan 51,800 na man diesel.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply