Hedikwatar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa jiragen sama na rundunar sojin kasar sun kai hare-hare tare da lalata kayayyakin ‘yan ta’adda a sansaninsu da ke garin Bukar Meram na kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno.
John Enenche, mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta kasa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a Abuja.
Enenche ya ce rundunar sojin ta tarwatsa ‘yan ta’adda da dama a garin Dole da ke kudancin jihar.
