Home Sabon Labari Sokoto: Gina furamare da ‘kasa’ don gwamnati ta gaza

Sokoto: Gina furamare da ‘kasa’ don gwamnati ta gaza

82
0

Al’ummar Runjin Dutsi da ke gundumar Sanyinnawal a Karamar Hukumar Shagari ta jihar Sakkwato sun sha alwashin gudanar da aikin gayya don samar da makarantar Firamare da ‘yayansu za su rika karatu a ciki.

Su dai mutanen wannan kauye sun yi zargin cewa babu irin roko da kuma kuka da ba su yi ba ga gwamnati na ganin an gina wa ‘yayansu makaranta, amma shiru, lamarin da ya kai su ga daukar wannan matakin na aikin-gayya a tsakanin su don samar da wannan makarantar Firamaren ga ‘yayan nasu.

Dama dai tun hawan gwamnatin jihar Sakkwato a shekarun 2015 ta kaddamar da dokar ceto fannin ilimi a baki dayan jihar, amma kawo yanzu masu sharhi na bayyana kwalliya ba ta kai ga biyan kudin sabulu ba.

Kawo lokacin hada wannan rahoto gwamnatin jihar ba ta kai ga fitar da matsayarta a kan irin wannan aikin gayyaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply