Home Labarai Sokoto: Gwamna Tambuwal ne ya yi nasara a Kotun Koli.

Sokoto: Gwamna Tambuwal ne ya yi nasara a Kotun Koli.

85
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

Daruruwan magoya bayan gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ke ci gaba da nuna farin cikinsu dangane da yadda gwamnan ya samu nasara a kotun koli a kan abokin hamayyarsa Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC.

Gwamna Tambuwal dan jam’iyyar PDP sun Kara ne da tsohon mataimakinsa Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC mai adawa a jihar.

Dama dai gwamnan sun sha zaunawa kotu kusan sau biyu inda wannan nasarar ta kotun koli ta kara tabbatar da shi ne zababben gwamnan jihar Sakkwato.

Tsananin tsoro da fargaba da ake da ita ya sanya Rundunar ‘yan sanda girke jami’anta dubu daya don dakile duk wata barazana da ka iya tasowa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply