Home Labarai Sokoto: Kotu ta soke zaben Sanata da Dan Majalisar Wakilai na APC

Sokoto: Kotu ta soke zaben Sanata da Dan Majalisar Wakilai na APC

120
0

Kotun daukaka kara da ke yankin Sokoto ta soke nasarar da hukumar zabe ta ba Alhaji Abubakar Shehu Tambuwal mai wakiltar Sokoto ta Kudu a matsayin Sanata da Dan majalisa Aliyu Shehu mai wakiltar Bodinga/Dange-Shuni/Tureta.

Tun da farko PDP a jihar ta ruga kotun sauraren kararrakin zabe inda ta kalubalanci nasarar APC a wadannan kujeru, amma kotun ta bayar da nasara ga APC.

Sai dai ranar Larabar nan alkalin kotun daukaka kara Frederick Oho ya soke zaben APC ya kuma tabbatar da nasara ga yan takarar jam’iyyar PDP.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya-NAN- ya ce kawo yanzu cikakken hukuncin bai fita ba, amma kotun ta ce za ta fitar da shi nan bada jimawa ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply