Home Labarai Sokoto: Mahukumta sun dawo da jarabawar MOCK kafin rubuta WAEC bayan shekaru...

Sokoto: Mahukumta sun dawo da jarabawar MOCK kafin rubuta WAEC bayan shekaru 10

84
0

Hukumomin da ke kula da samar da Ilimi a jihar Sakkwato sun ce sun shirya tsaf don soma rubuta jarabawar Mock ga dalibai ‘yan ajin karshe na Sakandare a duk fadin jihar.

Ana sa ran kusan dalibai ‘yan Sakandare dubu ashirin da biyar ne za su zauna jarabawar, zana jarabawar wani mataki ne ga share fagen rubuta babbar jarabawar kammala makaranbtar Sakandire WAEC da kuma NECO a Nijeriya.

Mahukuntan sun kuma sha alwashin duk dalibin da ya kasa cin jarabawar ta Mock to ba za’a iya masa rijistar rubuta WAEC da NECO ba.

To amma kuma ga alama hakan ya sosa zukatan iyayen yara dama wasu yaran akan daukar wannan matakin da hukumomin suka yi inda suke fargabar kada abun ya koma cuwa-cuwa.

Dama dai wannan jarabawa ta Mock an shafe sama da shekaru goma batare da ‘yan ajin karshe na Sakandare sun zana ta ba, amma sai gashi kwatsam an dawo da tsarin anan jihar Sakkwato.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply