Home Labarai Solar: Gidaje milyan 5 za su amfana a Nijeriya

Solar: Gidaje milyan 5 za su amfana a Nijeriya

207
0

Gwamnatin Nijeriya ta jaddada aniyarta ta samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana domin samar da ci gaba mai dorewa a fadin kasar.

Mr Laolu Akande wanda shi ne babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a ya tabbatar da haka a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Nijeriya da ke Abuja.

Ya kuma yi bayanin cewa akwai wani tanadin da gwamnatin kasar ke yi kan yadda gidaje miliyan biyar za su amfana da makamashin hasken ranar domin a kara inganta samuwar hasken wutar lantarki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply