Home Labarai Soyayya ta shiga tsakanin Nafisa Abdullahi da Ali Nuhu?

Soyayya ta shiga tsakanin Nafisa Abdullahi da Ali Nuhu?

94
0

Zaharaddeen Umar/AGJ

Jaruma Nafisa Abdullahi ce dai ta shirya fim din na “Buri Na” kuma ta fito a matsayin jaruma.

A hirar ta jaridar “Blueprint” ta ce tun a lokacin da take rubuta gundarin shirin ta yi tunanin zaben jarumi wanda zai iya isar da sakon da ke a cikin takarda ba tare da matsala ba. Kuma ta gamsu Ali Nuhu zai iya sauke wannan nauyin.

Hotan Nafisa Abdullahi da Ali Nuhu

Fim din ya nuna yadda Nafisa Abdullahi ta lalata soyayyar Ali Nuhu da wata ‘yar’uwarta ta jini ta kuma yi amfani da kafafen yada labari ta bata masa suna daga karshe ma ta sanya gawa a cikin motarsa duk dai domin ya shiga tarkonta. A karshe dai ta yi masa tayin ya yadda ya aure ta sai maganar ta wuce ta rufa masa asiri.

Jaruma Nafisa ta ce daga nan ta yi sa’a Ali Nuhu ya yadda suka yi aure. Ta ce a matsayin ta na furodusa ta zabi su yi soyayya da Ali Nuhu a fim din domin dogo ne kuma baki a kalar fata mai kyau kamar ta. Ta ce Ali Nuhu kyakykyawa ne da duk wata mace a masana’antar kannywood za ta so ta yi fim da shi.

Ali Nuhu fitaccen jarimin fim a kasar Hausa

Sai dai wadannan siffatau da Nafisa Abdullahi ta ba Ali Nuhu sun sanya jama’a da dama zargin akwai wata a kasa, abin da ya sa ke nan dan jaridar Blueprint ya tambaye ta, shin wannan ya tabbatar da zargin soyayyar da ake yi cewa kuna yi da Ali Nuhu ke nan?

Amma sai Nafisa Abdullahi a cikin raha ta ce” wannan maganar ku ce ta ‘yan jaridu, domin Ali Nuhu mai gida na ne kuma yana da matarsa suna zaman lafiya. Amma a cire maganar wasa, idan namiji kamar Ali Nuhu zai zo ya neme ni da aure toh ba zan yi jinkirin amsa masa ba kuma zan yi azumin kwana 30 domin godiya ga Allah”
Ta kara da cewa

” Idan mace ta sami kamar Ali Nuhu a matsayin miji, ka ga dai yana da tsawo ga bakar fata mai sheki ga ilimi da dukiya kuma yana da sakin-fuska ga kuma kyauta, to mai za ta jira in ba ta ci gaba da bautar Allah da kyautata ma mijinta ba”.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply