DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKasuwanciSpain na iya rasa kashi 30% na kyautar dala miliyan 50 ta...

Spain na iya rasa kashi 30% na kyautar dala miliyan 50 ta gasar Kofin Duniya saboda harajin Amurka

Rahotanni sun ce ƙasar Spain na iya rasa kusan kashi 30 cikin 100 na kuɗin kyautar dala miliyan 50 da ta samu bayan lashe gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, sakamakon harajin gwamnatin Amurka.

A ƙarƙashin dokokin harajin Amurka, kuɗin shiga da ’yan wasa daga ƙasashen waje suka samu ta hanyar ayyukan da suka gudanar a Amurka na iya fuskantar harajin tarayya da ya kai kashi 30 cikin 100 a kasar.

Jaridar Punch ta ruwaito kasar Spaniya ta lashe gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan ta doke Argentina da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka gudanar a filin wasa na New Jersey Stadium da ke New York ranar Lahadi, 19 ga Yuli.

A cewar FIFA, zakarun gasar za su karɓi dala miliyan 34 daga cikin jimillar dala miliyan 871 da aka ware a matsayin kuɗin kyaututtuka ga ƙungiyoyin ƙasashe 48 da suka halarci gasar.

Tuni dai wasu ’yan majalisar dokokin Amurka, ciki har da Tim Burchett da Jonathan Jackson, sun soki yiwuwar cire harajin kashi 30 cikin 100 daga kuɗin da ’yan wasan ƙasashen waje suka samu.

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin wasanni, William Copus, ya yi ikirarin cewa ’yan wasa na iya fuskantar ƙarin harajin jihohi a wuraren da suka buga wasannin ko kuma suka yi atisaye.

Wani bangare da masana ke hasashen zai iya ƙara yawan kuɗin harajin da za a cire daga abin da suka samu a gasar ta bana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata