[cmsmasters_row data_shortcode_id=”ebncgw3srh” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”q3q9prim5″ data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”skbvcq6str” animation_delay=”0″]
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce Raheem Sterling zai iya samun damar kai matsayin da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka kai.
Sterling ya taka muhimmiyar rawa a wasanni biyu da kasar Ingila ta buga a makon nan.
Shi ma kocin tawagar kasar Ingila Gareth Southgate ya ce Raheem Sterling dan wasa ne da ke da hazaka kuma yana da kwazon da zai iya zama kamar Messi da Ronaldo in har ya mayar da hankali.
“Za mu yi iya bakin kokarinmu na ganin mun taimaka masa, na san tabbas zai iya amma ba zan iyakance ma sa yadda zai yi ba, a gaskiya ina so ya zama hakan.” Inji Guadiola.
Sterling ya ci kwallaye 8 ringis a cikin wasanni 8 da ya buga wa kulob din sa da kuma kasarsa ta haihuwa wasanni a shekarar bana.
[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]
