Home Labarai Subul-da-baka: Mailafiya na wasan buya da jami’an tsaro

Subul-da-baka: Mailafiya na wasan buya da jami’an tsaro

122
0

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Dakta Obadiah Mailafia ya garzaya babban kotun da ke jihar Plateau domin neman a kare masa hakkinsa na walwala da adalci bayan da ‘yansanda suka gayyace shi zuwa Abuja.

Jaridar Muryar ‘Yanci ta yi hasashen cewa gayyatar da ‘yansanda suka yi wa Mailafia ba za ta rasa nasaba da gayyatar da Hukumar ‘yansandan ciki DSS, ta yi masa ba a kan ikirarin da ya yi na cewa wani gwamnan Arewa na cikin shugabannin Boko Haram.

Da ya ke jawabi ya yin taron manema labarai a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, Mailafia ya ce gayyatar da aka yi masa bita-da-kulli ne, cin mutunci, cin zarafi da yunkurin a bashi tsoro.

Ya bayyana cewa zai shigar da kara a kotu domin kalubalantar gayyatar da rundunar ‘yansandan ta yi masa.

A rahoton baya-bayan nan, an ruwaito cewa Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta aike wa Dakta Mailafia takardar gayyata zuwa Abuja. Ƴan sandan za su fara binciken su ne duk da cewa hukumar ƴansandan ciki, DSS, tana gudanar da nata binciken a kan zargin da tsohon mataimakin gwamnan CBN ɗin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply