Home Labarai Gwamnatin Nijeriya za ta rufe filin jirgin saman Enugu

Gwamnatin Nijeriya za ta rufe filin jirgin saman Enugu

67
0

Daga Nuruddeen Ishaq Banye

 

Hukumar kula da filayen jiragen saman Nijeriya FAAN, ta sanya ranar 24 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta rufe filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu har sai abun da hali ya bada.

 

Wata sanarwa da shugabar shashen al’amuran yau da kullum ta hukumar, Mrs Henrietta Yakubu ta fitar a Lagos, ta ce za a rufe filin jirgin ne domin samun damar yin wasu gyare-gyare kan hanyoyin saukar jirage.

Hoton wata hanyar saukar jirgin sama

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa rufe filin jirgin zai taimaka wajen magance wasu matsaloli da suka shafi tsaro da kula da lafiya.

 

Yakubu, ta ce za a sanar da ranar da za a sake buɗe filin jirgin a nan gaba, bayan an rufe shi da misalin ƙarfe 12am na daren ranar 24 ga watan Agusta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply