Home Sabon Labari Sulhu a Zamfara: Tsohon gwamna Yari ya tabka kuskure- Alhaji Murtala Shinkafi

Sulhu a Zamfara: Tsohon gwamna Yari ya tabka kuskure- Alhaji Murtala Shinkafi

99
0

Alhaji Murtala Shinkafi, mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara akan harkar tsaro a karamar hukumar Shinkafi a tattaunawarsa da jaridar DCL Hausa a safiyar litinin din nan ya ce kawo yanzu sama da mutum 300 sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar jihar Zamfara. Ya ce wannan ya biyo bayan shirin sasanci da sabon gwamnan jihar ya fito da shi.

Alhaji Murtala ya ce kalaman tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari da ya shaidawa BBC Hausa cewa bai kamata a yi sulhu ba,  kuskure ne. Y ace  shi Abdul-Aziz Yari bai dauki matakan sulhun da suka kamata ba a lokacin sa dalilin da ya sa ke nan sulhun da ya yi da ‘yan bindiga bai haifar da da-mai-ido ba.

Mai ba gwamnan jihar Zamfara shawarar ya ce akwai bukatar tsohon gwamna Abdul Aziz Yari ya shigo karkarar jihar Zamfara domin ya ga irin gagarumar nasarar da ake samu a sanadiyyar sulhun da sabon gwamnan ya fito da shi.

Ya ce a yanzu sun yi makonni uku ba tare da sun sami hare-hare na tashin hankali ba a yankin Shinkafi sabanin halin da tsohon gwamnan ya bar jihar na abin day a kira tashin-hankali.

 

Saurari Muryar Alhaji Murtala shinkafi a nan kasa

DOWNLOAD NOW

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply