Home Sabon Labari Sulhu:Gwamnan Sokoto Ya Mika Wa Yan Sanda Makaman Da Ya Karba A...

Sulhu:Gwamnan Sokoto Ya Mika Wa Yan Sanda Makaman Da Ya Karba A Hannun ‘Yan Bindiga

66
0

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya mika makamai dari da biyu ga rundunar’yan sandan jihar Sakkwato

Biyo bayan wani sulhu na sirri da ya gudana a tsakanin gwamnatin jihar da ‘yan bindingar da ke kai hare-haren ta’addanci a yankunan karkara na jihar Sakkwato.

Gwamna Tambuwal tare da yan sanda a lokacin mika musu makaman da yan bindiga suka mika don radin kansu

Wannan sulhun dai duk da yake ba a bayyane aka yi shi ba ana ganin idan ya tabbata to kam za’a samu zaman lafiya a jihar Sakkwato.

Gwamna Tambuwal a lokacin bikin hannanta makaman zuwa ga rundunar ‘yan sandan jihar ya ce shirin afuwa da yin sasanci na zama hanya mai kyau da idan jihohin Zamfara da Katsina da Kebbi suka rike shi da muhimmanci zai kawo karshen ta’addanci a jihohin.

 

Tambuwal ya yi kira ga ‘yan uwansa gwamnonin wadannan jihohin da su fito da tsari mai dauke da abubuwan da za su iya jan hankalin kidinafas da bandis su daina abubuwan da suke aikatawa su rungumi zaman lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply