Home Kasashen Ketare Sun haifi ‘ya’ya 10, bai taba ganin fuskar matarsa ba cikin shekaru...

Sun haifi ‘ya’ya 10, bai taba ganin fuskar matarsa ba cikin shekaru 47

306
0

Abin zai zamo banbarkwai idan aka ji cewa wasu ma’aurata sun kwashe shekaru 47 da yin aure amma mijin bai taba ganin fuskar matar ba.

Kari dadin-gushi ma har su na da ‘ya’yansu 10 bayan auren, amma mijin bai taba ganin fuskar matar ba har yanzu.

A labarin da jaridar “Lifeinsaudiarabia” ta wallafa ta ce dajjiton ya bayyana cewa matar tana irin ra’ayin nan mutanen dauri (gurguzu).

Dattijon yace matarsa ba ta son nuna masa fuskarta, don haka shi ma bai tilasta mata ba, ya bar ta da ra’ayinta.

Jaridar ta wallafa cewa cewa dama akwai irin wannan al’ada a kasar Saudiyya, da mace ke boye fuskarta ga namiji ko da kuwa mijinta ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply