Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma’aikatan sa.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya tabbatar da naɗin na Gambari a zaman majalisar zartaswar tarayya na yau Laraba.
Tun da farko dai, Gambari ya shigo fadar shugaban ƙasar da misalin ƙarfe 10:53am na safiyar yau.
Gambari, wanda ɗan asalin jihar Kwara ne, y gaji marigayi Abba Kyari, wanda ya rasu sakamakon cutar Covid-19.
