Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce babba sufeton yansanda na kasa Muhammad Adamu ya amince da a kara jibge jami’an yansanda a jihar don yakar ta’addanci.
A cikin wata takarda daga Darakta Janar na watsa labaran gwamnan Yusuf Idris, ya ce gwamnan Matawalle ya samu wannan amincewar ne a lokacin da ya kai ziyara a ofishin babban sufeton yansanda da ke Abuja.
