Home Kasashen Ketare Ta’addanci: Buhari Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma A Kasar...

Ta’addanci: Buhari Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma A Kasar Burkina Faso

73
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”cc4hcxdvov” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”q17kekuj5o” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”07dfm4z49″ animation_delay=”0″]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a yau Asabar domin halartar zaman tattaunawa na yini guda da shugabannin kasashen Afirka ta Yamma wadanda ke  a karkashin kungiyar Ecowas za su gudanar akan yadda za’a kawo karshen ta’addanci a wannan yanki. .Zaman dai za’ayishi a Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso.

 

Ganin yadda aikin ta’addanci ke kara karuwa da fadada a ko’ina acikin yankunan kasashen Afrika ta yamma, shi yasa shugabannin suka kira taro don a zauna a sake duba al’amurran tsaro, da kuma sake kirkiro wasu sabbin dabaru don shawo kan matsalar hare-hare da ake kai wa a yankunan.

 

Bayanin da ya fito daga bakin mai bawa shugan kasa shawara akan harkar sadarwa Chief Femi Adesina ya ce,wannan zama da za’ayi tuni aka yanke shawarar yin shi a zaman da shugabannin kasashen Afrika ta yamma suka yi karo na 55 da aka yi  ranar 29 ga watan Yuni 2019 a karkashin kungiyar Ecowas .

Shugaba Buhari na Nijeriya

Jaridar The Nation ta ce Shugaba Buhari, acewar mai magana da yawunsa ya gamsu da hadin gwiwar da akayi akan yaki da ta’addanci, kuma yasha alwashin ci gaba da hadin gwiwar a karkashin kungiyar ta Ecowas dama wasu kungiyoyi na kasa da kasa domin shawo kan matsalar.

 

A zaman da za’ayi a Ouagadougou, shugabannin kasashen Afrika ta Yamma suna saran daukar muhimmin mataki da kyakyawan shiri domin yaki da ta’addanci, kuma suna son a rinka bibiyar matakan da za’a dauka don ganin an ci gaba da aiwatar dasu don tabbatar da zaman lafiya a yankunan.

 

Shugaban kasa Buhari za ya samu rakiyar wasu daga cikin gwamnoni kamar su; Abubakar Bello da Dapo Abiodun da Okezie Ikpeazu na jihohin  Niger,Ogun da Abia. Akwai kuma mininstan kula da harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai murabus,da dai sauransu .

 

Ana sa ran shugaban kasar ya dawo a Abuja da zaran an kammala taron.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply