Home Sabon Labari Ta’addanci: Gwamna Masari da Gwamna Matawalle da Gwamna Tambuwal sun nemi agajin...

Ta’addanci: Gwamna Masari da Gwamna Matawalle da Gwamna Tambuwal sun nemi agajin Jamhuriyar Nijar

68
0

Yakuba Umaru Maigizawa, Damagaram Nijar

 

A ranar Lahadin nan ne aka kammala wani taro tsakanin gwamnan Maradi Zakkari Oumarou da wasu takwarorinsa guda Uku(3) na tarayyar Nijeria da suka hada da na Katsina, Sokoto da kuma Zamfara dukkansu dake da iyaka da jihar ta Maradi.

Gwamna Zakari Oumarou na jihar Maradi Nijar mai masaukin baki

Taron da aka bude a ranar Asabar dai ya maida hankali ne bisa kan batun tsaron kan iyakokin jihohin da suke fama da matsalar ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane dan neman kudin fansa.

A yayin jawabin shi na bude taron a ranar Asabar mai masabkin bakin Malam  Zakkari Oumarou a yayin jawabinsa na maraba ya yi kira ga al’ummomin yankin nasu da su bada hadin kai ga jami’an tsaro wajen yakar ‘yan ta’addar yankin.

Sabon Asibitin Maradi da Gwamnonin suka ziyarta

Ko baya ga batun tsaro ma taron na kwanaki biyu(2) ya tabo batun ‘yan gudun hijira da ke zaune a sansanoni daban-daban  inda a yanzu haka jihar ta Maradi ke kula da ‘yan gudin hijirar kimanin dubu ashirin(20,000) da suke fitowa daga jihohin uku(3) da ke da iyaka da jihar Maradi.

 

Maigizawa/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply