Home Labarai Ta’addanci: sojoji sun kafa sansanoni a dajin Birnin Gwari

Ta’addanci: sojoji sun kafa sansanoni a dajin Birnin Gwari

93
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya karkashin jagorancin Air marshal Sadiq Baba Abubakar ta gudanar da wani bikin bude gidajen wucin-gadi da zai taimaka mata wajen yakar yan ta’adda a yankin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.

Air Marshal Sadiq Abubakar shi ne ya jagorancin bikin na kaddamar da gidajen ya kuma bayyana cewa rundunar tana kokari wajen ganin ta samar da zaman lafiya a dukkanin sassan da ke fama da matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa hukumar ta samar da gidajen wucin-gadin ne domin samun damar yakar ‘yan bindiga da suka addabi jama’ar wannan yanki dama makwabtansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply