Home Labarai Ta’addanci: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 22 a jihar Sakkwato

Ta’addanci: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 22 a jihar Sakkwato

74
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

Da yammacin jiya Laraba n wasu ‘yan bindinga bisa babura dauke da muggan makamai suka kaddamar da hare-hare a wasu kauyukka sama da biyar da ke cikin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Maharan sun kora dabbobi da dama da kuma cinna wa garuruwan wuta lamarin da ya sa kowa ya fito saboda zafin wuta sai su harbe shi.

Jaridar DCL Hausa ta tattauna da wani da ya nemi da a sakaya sunansa, inda yace sun kashe mutane sama da talatin sun Kuma kone motoci shidda.

To amma a ta bakin Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad Abubakar Sadiq yace mutane 22 ne aka kashe.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga garuruwan ne da kakin sojoji. Garuruwan da abin ya fi shafuwa sune garin Gangara da DantaSakku da Kube, wadanda yanzu haka mutanen wadannan yankuna suna cikin halin fargaba.

Shaidar gani da idon ya ce, ‘yan bindigar sun dirar wa garuruwan ne tun misalin karfe 4 na yamma, amma sai zuwa karfe 7 suka kammala.

Yace duk da kasancewar sojoji a yankin amma ba sa iya shiga yankin da maharan ke ta’asar su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply