Home Sabon Labari Ta’addanci: Za a saki ‘yan bindiga 100 a jihar Zamfara

Ta’addanci: Za a saki ‘yan bindiga 100 a jihar Zamfara

67
1

Daga Abdullahi Garba Jani

Gwamnatin jihar Zamfara ta ayyana shirinta na sakin wasu ‘yan bindiga kimanin 100 daga gidan yarin jihar ta bisa yarjejeniyar sasancin da aka cimmawa tsakani a jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa ana zargin ƴan bindigar ne da kitsa wasu hare-hare tare da aikata laifukan ta’addanci a jihar, inda yarjejeniyar ta cimma cewa za a sake su kafin makon nan ya kare.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zailani Bappa ya fitar, ta ambato Gwamna Bello Matawalle na nuna rashin jin daɗin sa ganin yadda ayyukan ta’addanci ke ci gaba da mamaye wasu yankuna na Arewa maso yammacin Nijeriya.

Gwamna Bello Mulohammed na jihar Zamfara

Idan za a iya tunawa dai a baya an samu zaman doya da manja tsakanin Fulani Makiyaya da manoma wanda ake ganin shi ne matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a jihar, wadda ke Arewa maso yammacin Nijeriya.

A shekarar 2016 ma, jihar Katsina da ke maƙwabtaka da Zamfara ta aiwatar da irin wannan tsari na zaman sasanci inda aka sulhunta da manyan ƴan bindiga na jihar, har aka samu sauƙin tashe tashen hankula, saidai wasu na ganin wannan sulhu ya taɓarɓare ne ta dalilin rashin aiwatar da shi a jihohi maƙwabta.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin tufka ce da ta kamata a yi wa hanci tun wuri, ba sai an bari lamari ya kai ga gagarar kundila ba, cike da fatar cewa zaman sulhun da ake ciki, ya haifi ɗa mai ido.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

 1. Hi! dclmedia24.com

  We make available

  Sending your message through the feedback form which can be found on the sites in the contact partition. Contact form are filled in by our application and the captcha is solved. The profit of this method is that messages sent through feedback forms are whitelisted. This technique improve the chances that your message will be read.

  Our database contains more than 25 million sites around the world to which we can send your message.

  The cost of one million messages 49 USD

  FREE TEST mailing of 50,000 messages to any country of your choice.

  This message is automatically generated to use our contacts for communication.

  Contact us.
  Telegram – @FeedbackFormEU
  Skype FeedbackForm2019
  Email – FeedbackForm@make-success.com
  WhatsApp – +44 7598 509161

Leave a Reply