Home Labarai Taimakon ƴan bindiga: Ƴan sanda sun kama na hannun daman Yari

Taimakon ƴan bindiga: Ƴan sanda sun kama na hannun daman Yari

185
0

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kama wasu magoya bayan jam’iyyar APC 17 ciki har da Muhammadu Abubakar Ɗantabawa, wani na hannun daman tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari.

An dai kama su ne bisa zargin ganawa da wasu tubabbun ƴan bindiga, da nufin sake mayar da su cikin harkar.

Magoya bayan jam’iyyar dai sun fito kan tituna don yin zanga-zangar rashin amincewarsu da wannan mataki, yayin da ƴan sanda suka tarwatsa su da barkonon tsohuwa lokacin da suka yi yinƙurin shiga shelkwatar ƴan sandan.

A wata sanarwa da ya fitar, Kakakin Rundunar ƴan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya ce an kama mutanen ne bisa bayanan sirri da suka samu a kan su, sannan ya ƙaryata cewa akwai siyasa a cikin batun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply