Home Coronavirus Takaita zirga-zirga zai hana yaduwar corona a Nijeriya – MDD

Takaita zirga-zirga zai hana yaduwar corona a Nijeriya – MDD

60
0

Majalisar dinkin duniya tace muddin aka takaita zirga-zirga a Nijeriya, za a samu saukin yaduwar cutar corona a kasar.

A rahoton rubu’i da majalisar dinkin duniyar ta fitar, ta shawarci gwamnatin Nijeriya da ta duba yiwuwar hana zirga-zirga domin rage yaduwar cutar corona a yankuna.

Rahoton yace yawaitar zirga-zirga da cudanya tsakanin mutane, babu ko shakka na taimakawa sosai wajen yada corona.

A rahoton an ba da shawarar cewa mutane su rika killace kansu, da sauran bin matakan kare kai daga kamuwa ko yada cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply