DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeSiyasaTakarata da Peter Obi ta fi ta sauran ‘yan takara cancanta a...

Takarata da Peter Obi ta fi ta sauran ‘yan takara cancanta a zaɓen 2027- Kwakwaso

Ɗan takarar mataimakin shugabancin Nijeriya NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa haɗin gwiwarsa da Peter Obi ya fi sauran tikitin takara ƙarfi, cancanta, ƙwarewa da amincewar jama’a a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira da Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a Abuja.

Tsohon Gwamnan Kano ya ce haɗin gwiwar Obi da shi zai iya kayar da duk wani ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, saboda yana haɗa tasirin siyasar arewacin Nijeriya da kuma ƙaƙƙarfan goyon bayan da Obi ke da shi a kudancin ƙasar.

Kwankwaso ya ce an samar da tikitin ne domin samar da daidaito da kuma haɗa kan ’yan Nijeriya ba tare da la’akari da bambancin yanki ko addini ba.

Ya ce: “Babu wani ɗan takara da zai iya doke namu wajen cancanta, ƙwarewa da kuma kishin ƙasa.”

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwarsu ya fi sauran ’yan takara ƙarfi wajen nuna tausayi ga talakawan Nijeriya da ke fama da matsin rayuwa.

Kwankwaso ya ce ƙwarewar da ya samu a zaɓen 2023 ta taimaka masa wajen fahimtar Peter Obi sosai, abin da ya tabbatar masa da cewa za su iya yin aiki tare domin kawo sauyi a ƙasar.

Ya ce Nijeriya na buƙatar sauyi saboda ƙalubalen rashin tsaro, talauci, lalacewar ababen more rayuwa da kuma matsalolin da manoma ke fuskanta.

Tsohon gwamnan ya kuma ce cire tallafin man fetur bai haifar da inganta rayuwar ’yan Nijeriya yadda ake tsammani ba, yayin da manoma ke fuskantar matsala sakamakon shigo da kayan abinci masu rahusa daga ƙasashen waje.

Kwankwaso ya bayyana cewa haɗin gwiwar kungiyar Kwankwasiyya, NDC da magoya bayan Peter Obi na da nufin kawo sauyin siyasa ta hanyar dimokuraɗiyya, irin wanda ya faru a zaɓen 2015.

Ya ce haɗin gwiwar ya ginu ne bisa adalci, gaskiya da daidaito, tare da kudurin inganta rayuwar al’ummar Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata