Home Labarai “Takaru” 384 sun isa Abuja daga Saudi Arabia

“Takaru” 384 sun isa Abuja daga Saudi Arabia

50
0

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje ta sanar da dawowar wasu ‘yan kasar su 384 daga kasar Saudiyya.

Wadanda suka dawo din suna daga cikin ‘yan Nijeriya guda 802 da gwamnatin Nijeriya ta alkawarta cewa za a kwasho su zuwa Nijeriya a ranakun Alhamis da Juma’a.

Ma’aikatar harkokin waje ta kasar ta bayyana cewa rukuni na biyu na sauran wadanda suka rage din, zai iso kasar ne a ranar Juma’a kuma jami’an na ma’aikatar za su karbe su a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na Kasa da Kasa, Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply