Home Labarai Talauci ya haddasa rashin kyakkyawan tsarin lafiya a Nijeria – NHIS

Talauci ya haddasa rashin kyakkyawan tsarin lafiya a Nijeria – NHIS

110
0

Babban sakataren Inshorar Lafiya na Nijeriya NHIS Farfesa Muhammed Sambo ya ce talauci ya taka rawa wajen rashin inganta tsarin kiwon lafiyar kasar.

Farfesa Sambo wannda ya yi magana wajen wani taro kan Covid-19 da Media Trust ya shirya a ranar Alhamis, ya ce bangaren kiwon lafiya na fama da matsaloli musamman rashin samun wadatattun kudade.

Ya ce ba a ware wa bangaren isassun kudi a kasafin kudi saboda yadda ake bukatar kudin a wasu bangarori kuma ga karancinsu.

Ya kuma kara da cewa rashin kyakkyawan tsarin yadda za a tafiyar da kudaden kungiyoyin bada taimako shima ya taimaka wajen rashin ci gaban bangaren.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply