Home Labarai Tallafin N220bn: Kananan ‘yan kasuwa sun koka da tsarin CBN

Tallafin N220bn: Kananan ‘yan kasuwa sun koka da tsarin CBN

71
0

‘Yan kasuwa sun koka kan tafiyar hawainiyar rabon kudin tallafin da babban bankin Nijeriya ya ba masu kanana da matsakaitan sana’o’i na Naira Biliyan 220.

Da yake Magana a wajen wani taron karawa juna sani da aka shiryawa mata a Abuja shugaban cibiyar ciniki da masana’antu ta Abuja Prince Adetokunbo Kayode ya ce tsaikon da ake samu wajen rabon kudaden ya sanya wadanda za su amfana da su har yanzu ba su same su ba.

Ya ce tun lokacin da ya fara aiki a matsayin shugaban cibiyar babu wani daga cikin jama’ar sa da ya amfana da wadannan kudade.

Ya ce kokarin raba kudin tallafin kasuwanci ta hanyar bankunan ‘yan kasuwa bai yi armashi ba, domin ba su da shirin bada kudin ga kananan ‘yan kasuwar.

Ya kara da cewa saboda wahalar da ake sha wajen samun kudaden tallafin ne, ya sanya cibiyar sa ta bullo da wasu hanyoyin samar da kudaden da za ta tallafawa ‘yan kasuwar ta su inganta kasuwancin su.

a nata jawabin shugabar kungiyar cibiyoyin masana’antu da zuwa jari ta Nijeriya NACCIMA, Hajiya Saratu Iya Aliyu, ta yabawa babban bankin na CBN da ya ware kashi 60 cikin dari na kudaden ga mata ‘yan kasuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply