‘Yansanda a jihar Neja sun ce wata tankar dakon mai daga birnim Minna zuwa Suleja, ta kwace ta kutsa kai cikin masallaci a Lambata cikin karamar hukumar Gurarar ta jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Adamu Usman ne ya tabbatar da faruwar lamarin a birnin Minna.
Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na daren Lahadi, da hakan ya yi sanadiyyar konewar wasu motoci da kuma ita kanta tankar da shaguna da sauran ababen bukata.
