Daga Abdullahi Garba Jani
A ranar Larabar nan, hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Wukari jihar Taraba, Nijeriya ta sanar da rufe jami’ar ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta bada rahoton cewa hakan ta faru biyo bayan zargin sacewa da kashe wasu dalibai da malaman jami’ar ta dalilin rikicin kabilanci tsakanin kabilar Tiv da Jukun.
Magatakardar Jami’ar Mr Magaji Gangumi a cikin wata takarda yace hukumar gudanarwar jami’ar ce ta amince da rufe makarantar har zuwalokacin da al’amurra za su daidaita.Ya ce rufe makarantar ya zamo wajibi don ganin yadda dalibai suka barke da zanga-zanga bayan faruwar lamarin.
Daga bisani, shugaban jami’ar Farfesa Abubakar Kundiri, ya tabbatar da cewa an samar da tsauraran matakan tsaro don tabbatar da tsaron rayukan ma’aikata da daliban jami’ar, amma dai kowa ya tafi gida har sai al’amurra dun inganta.
Jihar Taraba dai na ci gaba da fuskantar rashin tsaro galibi saboda rikicin kabilanci da ke neman daidaita kabilun da suka taba zama a inuwa daya.
