Tsohon kyaftin ɗin Ingila, David Beckham, ya ce tarihin ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, zai ci gaba da wanzuwa har abada, bayan da ɗan wasan ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasar Argentina wasa.
Jaridar Punch ta ruwaito Messi mai shekaru 39 ya kawo ƙarshen taka leda a ƙasarsa ne bayan buga wasanni 207, inda ya zura ƙwallaye 125.
Ya kuma jagoranci Argentina ta lashe Kofin Duniya na 2022 a Qatar, yayin da wasan karshe da ya buga wa ƙasar ya kasance wasan da Argentina ta sha kashi a hannun Spain a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya a watan Yulin 2026.
Beckham, wanda a yanzu yake cikin masu mallakar ƙungiyar Inter Miami da Messi ke bugawa kwallo, ya ce duniya ta yi sa’ar kasancewa cikin waɗanda suka shaida gwanintar ɗan wasan tun yana ƙarami.
Ya ce Messi ya kasance abin koyi ga miliyoyin yara a Argentina da sauran sassan duniya, tare da yaba masa kan yadda ya bai wa ƙasarsa kyautar lashe Kofin Duniya.
