Home Taskar Guibi TASKAR GUIƁI: 20-05-2020

TASKAR GUIƁI: 20-05-2020

247
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da bakwai ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Majalisar Dattawa ta bukaci a fadada aikin sojojin da shugaban kasa ya ba su umarnin su tsaftace jihar Katsina, zuwa jihohin Kaduna, da Sakkwato, da Neja, da Zamfara, da Kabbi.

2. Majalisar Wakilai na cigiyar Canisawan nan goma sha biyar da aka ce sun zo ne don taimakawa yaki da kwaronabairos, saboda ba a jin duriyarsu. Sai dai ministan cikin gida ya ce suna nan a cikin gida Nijeriya suna aiki.

3. Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA a takaice, ta zargi hukumomin tsaro da karbar cin-hanci wajen matafiya da ke karya dokar zirga-zirga daga jiha zuwa jiha.

4. Wata mai shekara ashirin da biyu da aka killaceta a Legas saboda jinyar kwaronabairos, ta haifi ‘yan biyu namiji da mace abinta tubarkallah.

5. Gwamnatin jihar Taraba ta ce ba ta da sauran mai kwaronabairos a jihar duk kowa ya warke.

6. An ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojojin Nijeriya a lokacin da suka yi kasassabar kai hari Dapchi da ke jihar Yobe.

7. Sashen DAC na jami’ar Ahmadu Bello Zariya sun soma ganin dilin-dilin bayan wata da watanni babu labari.

8. Kwamitin shugaban kasa na yaki da yaduwar miyagun cututtuka ya ce gwamnatin tarayya ta yi tanadin da dalibai za su iya karanta darussansu ta intanet wato e-learning, kuma kyauta ba ruwansu da sayen data. Tare da yin kira ga dalibai da lakcarori su kiyaye.

9. Gwamnatin jihar Nasarawa ta dage hanin gudanar da al’amuran addini na mako biyu.

10. Majalisar Wakilai ta ce ba ta ji dadi ba da ta ji tunda aka fara kaya-kayan kwaronabairos, ashe ba a biya ma’aikatan lafiya na Abuja albashi ba.

11. Babban Bankin Nijeriya ya ce yana shirin raba wani bashi naira biliyan hamsin ga talaka dubu dari uku da Allah Ya tsaga da rabonsa.

12. Babban Bankin Nijeriya ya bullo da wani tallafi ga ‘yan Nijeriya da ake kwasowa zuwa gida daga kasashen ketare, saboda idan an kawo su an jide su, akwai kudaden da akan bukaci su biya na killace su, da sauransu.

13. Yau akwai walwalar samun dalin-dilin ga ma’aikatan jihar Kaduna, da fita sayen kayan abinci a jihar Kaduna. Sai dai gwamna Nasir El-Rufai ya ce walwalar ta yau da gobe ce kadai, kuma ranar Sallah zai je ya tare kan iyakar Kano da Kaduna, Mataimakiyarsa za ta tare kan iyakar Katsina da Kaduna, Sakataren gwamnatinsa zai tare kan iyakar Abuja da Kaduna, don hana wani taho wa jihar Kaduna da tsarabar kwaronabairos.

14. Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar janye tallafin kudi da yake bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO idan nan da kwana talatin ba ta masa gamsasshen bayani a kan halin da ake ciki a kan kwaronabairos ba.

15. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, akwai mutane 226 sabbi da suka harbu da kwaronabairos a jihohi kamar haka:

Legas 131

Ogun 25

Filato 15

Edo 11

Kaduna 7

Oyo 6

Abuja 5

Adamawa 5

Jigawa 4

Ebonyi 4

Nasarawa 3

Bauci 2

Gwambe 2

Inugu 1

Bayelsa 1

Kowacce jiha na da :

Legas 2755

Kano 842

Abuja 427

Katsina 281

Barno 227

Bauci 224

Jigawa 205

Ogun 178

Kaduna 152

Oyo 153

Gwambe 136

Sakkwato 113

Edo 119

Zamfara 84

Kwara 65

Ribas 53

Oshun 47

Filato 50

Kabbi 31

Yobe 32

Nasarawa 34

Delta 27

Neja 22

Adamawa 26

Ondo 20

Ekiti 19

Akwa Ibom 18

Taraba 17

Inugu 16

Ebonyi 13

Imo 7

Bayelsa 7

Abiya 5

Anambra 5

Binuwai 5

Kogi 0

Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 6,401

Jimillar wadanda suka warke 1,734

Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 192

Jimillar da ke jinya 4,475.

Mu yi sahur lafiya, yini lafiya, buda baki lafiya.

Af! Jiya na yi aune da martanin da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayar a kan IPPIS kamar haka:

TARKON IPPIS YA KUSA FARA KAMU?

An fara da zabge albashin Malamai?

An soke daukar malaman ‘sabbatical’ da ‘visiting’ da ‘contract’ da ‘adjunct’, daga ciki ko wajen Nijeriya?

An soke alawus na VC da Mukarrabansa?

An soke alawus na ‘Deans’ da ‘HODs’ da sauran masu rike mukamai a jami’a?

An soke alawus na ‘external examination’ da ‘internal defence’ da ‘assesment’ na zama Dan Galadiman Farfesa da Farfesan?

An kawar da kudaden ‘moderation’ na jarabawa?

An hana bayar da alawus na duba digiri na 2 da na 3?

ME KUMA YA RAGE?

Saura a biyo da karin kudin makaranta da sauran kudaden gudanar da jami’o’i da dalibai da iyaye za su dinga biya duk shekara?

Sai kuma a shigo da tsarin ba dalibai bashi daga bankuna domin su biya kudin makaranta da sauran kudaden jarabawa da karatu da zai bautar da su a tsawon shekaru suna biya?

An rufe bakin tsanya, ASUU, idan muka kara jin pim daga bakin ASUU na cewa akwai matsaloli a jami’o’in kasar nan, domin ko komi ya yi daidai, sai kuma bugu da dauri?

“Allah ya isa?”

Oh, da ma akwai mai tababar Allan bai isa ba ne?

Prof. Malumfashi Ibrahim

Za kuma a iya ganin wannan labarun nawa na yau a dandalin twita na:

Is’haq Idris Guibi

Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply