Home Tsaro Taskar Guibi: 01.01.2021

Taskar Guibi: 01.01.2021

272
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, goma sha bakwai ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Yau aka shiga sabuwar shekarar 2021, sai dai ana shiga shekarar da minti daya, suka dauke wuta, sai wuraren karfe hudu na asubahin nan suka dawo da ita. Da ke nuna alamun talaka zai ci gaba da zama a duhu, da biyan kudin zama a duhun a shekarar nan ta 2021.

2. Yau da karfe bakwai na safiyar nan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabi kai tsaye na sabuwar shekarar 2021, sai dai da bakwan ta yi za ka ga an dauke wuta, da ba za ka iya ganin jawabin ta talabijin ba, sai ta rediyo.

3. Jiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudi na shekarar 2021, na naira tiriliyan goma sha uku da rabi da ‘yan kai ya zama doka. Ya hori hukumomin da ke tattara kudaden shiga, su dage don samar da kudaden tafiyar da kasafin na shekarar 2021. Sai dai hukumomin na korafin ta ya za su iya tara kudaden shiga daga jama’a da ke biyan kudin zama a duhu, maimakon samun wutar su yi sana’o’i don samun kudaden shiga da biyan gwamnati kudaden shiga?

4. Hukumar kwastam ta yankin Apapa/Afafa, ta kama kaya na wajen naira tiriliyan goma sha bakwai a ‘yan watannin nan. Sai dai na ji wasu ma’aikatan kwalejojin foliteknik da ke bin ariyas na sabon albashi, da a watan cita na Afrilu, sun cika shekara biyu ke nan suna jira, suna korafin sun ji labarin kudaden nasu gabadaya ba su wuce naira biliyan hudu ba, a sa kwastam ta sayar da kayan, gwamnati ta karbo biliyan hudu daga sha bakwan don biyansu.

5. Namadi Sambo ya leka Fadar Shugaban Kasa jiya, ya isar da sako ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan zaben kasar Nijar da aka yi na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.

6. Sojoji sun ce daga watan Maris na shekarar 2020 zuwa jiya sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram da ire-irensu su dubu biyu da dari hudu da ‘yan kai, suka kama dubu daya, da dari tara da goma. Sojojin sun kuma ce sun yi wa ‘yan kungiyar ISWAP luguden wuta ta sama, a yankin da ke kusa da tafkin Chadi.

7. Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe otel din Asher da ke Barnawa a cikin garin Kaduna, da ake zargin an shirya wata dabdala ta badala, da ashararanci tsakanin maza da mata.

8. Mutanen kauyen Guibi na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe kafin wa’adinsa ya kare.

9. A watan nan ake sa ran isowar magungunan rigakafin kwaronabairos Nijeriya.

10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos har mutum 1031 a jiya, da wasu ke danganta karuwar cutar ga cunkoson neman lambar shaidar dan kasa, da wasu ke zargin gwamnati ta iya rufe makarantu, da takaita yawan jama’a masu taruwa wajen ibada, har da cin tara in ba a sa takunkumi ba, amma ta tilasta wa jama’a cunkoso don neman lambar dan kasa. Ga alkaluman da jihohin:

Legas 570
Abuja 117
Kaduna 109
Nasarawa 34
Bauci 31
Kano 28
Filato 26
Sakkwato 26
Ogun 25
Ribas 16
Abuja 10
Imo 7
Taraba 6
Delta 4
Oshun 4

Jimillar da suka harbu 87,510
Jimillar da suka warke 73,713
Jimillar da ke jinya 12,508
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,289

* A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fita an jima da safe, don duba shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku, daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis

Mu wayi gari lafiya.

Af! A game da rushe otel din Asher da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi, ga daya daga cikin ra’ayoyin da na tsinto a fesbuk sai dai cikin harshen Ingilishi ne:

“On the Demolition of the Asher Hotel

Some people planned to host a sex party in a hotel in Kaduna. No doubt what they planned on doing is a great evil.

The state government, in response to their evil plan, demolished the building that was proposed to be the venue of the evil act. In my opinion, as a layman, what the state government did is a greater evil.

We are a democracy operating under the rule of law for goodness sake!

If what the evil planners planned on doing violates the laws of the land, I am not saying it doesn’t, the right thing for the state government to do is to charge them to court, and let a court of competent jurisdiction decides based on the laws of the land.

Bulldozer politics and bulldozer justice, or injustice, will, on the long run, never, as the Hausa people would say “haifa” for us all, the people and the government, a “ɗa mai ido”.

I hope the last paragraph makes some sense to the reader, especially the non Hausa speaking reader 😉

Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
31/12/20″

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply