Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 01.02.2021

Taskar Guibi: 01.02.2021

122
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Litinin, goma sha takwas ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Fabrairu, na shekarar 2021.

1. Jiya sabbin manyan hafsoshin tsaro na kasar nan suka leka jihar Barno, suka gana da gwamnan jihar Zulum, suka kuma leka harabar rundunar da ke ta fafatawa da Boko Haram da ake kira Operation Lafiya Dole Theatre Command. Sun ce sun je ne don ganin abubuwan da ke nan, da yin sabon shiri. Sai dai wasu bayanai na nuna ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kai wani sabon farmaki jihar ta Barno.

2. Sojoji a jihar Sakkwato, sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga su goma sha biyu, su kuma sun rasa soja daya a lokacin da suke fafatawa da ‘yan bindigan.

3. Wasu kidinafas a jihar Kogi sun kashe wata yarinya mai shekara shida Farida, da kuma wani mutum bayan an biya su kudin fansarsa.

4. Watan jibi na Afrilu, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu cur, suna dakon ariyas na sabon albashi.

5. Yau daya ga watan Fabrairu, dilin-dilin shiru musamman a manyan makarantu na gwamnatin tarayya.

6. A cikin wadanda suka bibiyi rubutuna na jiya, suka yi tsokaci, akwai Akilu Muhammad da ke cewa ” ___MUNA GODIYA AMMA JIYA CIKIN DARE A SAMAN ECWA KASUWAN MAGANI KIDINAFAS SUNYI AWON GABA DA MUTUM BIYU MRS. L GIWA DA WANI FASTO”

7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, da ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, kafin ya sauka.

8. Akwai sabbin harbuwa da kwarona, mutum 685, a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 355
Kaduna 58
Nasarawa 46
Kano 40
Akwa Ibom 33
Katsina 26
Ogun 25
Oshun 21
Ribas 16
Edo 15
Oyo 13
Ondo 12
Barno 11
Ekiti 9
Kabbi 3
Filato 2

Jimillar da suka harbu 131,242
Jimillar da suka warke 104,989
Jimillar da ke jinya 24,667
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,586.

9. Yau za a koma makaranta, firamare da sakandare da manyan makarantu, da su Islamiyya a jihar Kaduna.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wasu na ta radar ga Baba Buhari can na ta sabgar jam’iyyarsa ta APC a cikin jama’a a jihar Katsina, ba takunkumi ba tazara abinsa. Alhali ga doka can ya sa wa hannu ta daure talaka wata shida, ko tara, ko duka biyun, idan aka kama shi ba takunkumi, ko ba da tazara da sauransu. Ni ma dai na yi korafin ina ji wa Baba Buhari tsoron kada ya harbu da kwarona. Af watakila gwamna Yahya Bello na jihar Kogi, ya ba shi fahamin kwarona, da ya hana sauran gwamnoni ne!

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply