Home Taskar Guibi Taskar Guibi 01.05.2020

Taskar Guibi 01.05.2020

79
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, takwas ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Mayu na 2020.

1. Gwamnatin Tarayya ta ce ranar litinin da ma’aikata za su koma aiki, wadanda ke mataki na goma sha hudu zuwa sama ne za su je wajen aiki, da karfe takwas na safe su tashi karfe biyu. Kuma sau uku kawai a mako, litinin da laraba da juma’a. Ba yawan ganawa da baki a ofisoshin nasu, tare da kiyaye nesa-nesa da juna.

2. Mazauna Abuja sun yi korafin shinkafar da gwamnati ta raba musu a matsayin tallafi, ba ta da kyau, ga wari da hamami, ga buntu, ga gansakuka da burtuntuna da hunhuna.

3. Kungiyar Tarayyar Turai EU a takaice ta raba wa mutanen Abuja kayan abinci na daruruwan miliyoyin naira.

4. Likitoci da ke aiki da gwamnatin jihar Kaduna sun ce ba su yarda da kudadensu na albashi da gwamnatin ta yanke musu ba a matsayin tasu gudunmawar ga yaki da cutar kwaronabairos. Likitocin suka ce su ne ke karbar albashi kasa da duk sauran likitocin da ke kasar nan. Ga shi su ke ta kai komo a wannan lokaci ba hutu, sannan a yanke musu albashi. Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ma’aikatan jiha da albashinsu ke rage naira dubu sittin da bakwai bayan an cire haraji da sauransu ne aka yankewa albashin. Masu karbar kasa da haka ba a taba musu albashi ba.

5. A jihar Kano an kama mutum arba’in da biyar da ya saba wa dokar kulle. Haka nan an samar da wuraren gwajin gano masu cutar kwaronabairos a jihar har guda biyu. Daya yana jami’ar Bayero ta Kano.

6. Kwamitin shugaban kasa a kan yaki da cutar kwaronabairos ya koka a kan rashin isassun wuraren killace masu lalurar kwaronabairos a kasar nan, tare da rokon jama’ a da ke da gidajen da babu kowa a ciki, su ba da aro a dinga killace masu lalurar, musamman a Legas.

7. An bayyana cewa ma’aikatan lafiya guda dari da goma sha uku ne suka harbu da cutar kwaronabairos a kasar nan, yawancinsu suna aikin jinyar masu lalurar ne a asibitocin da ba a amince su yi jinyar masu lalurar ba.

8. Ana ta yunkuri daban-daban na gano maganin kwaronabairos a Nijeriya da kasashen ketare. A Nijeriya akwai Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutse, sai a jihar Yobe wani Dafta Jawa, sai Ooni na Ife, sai gwamnan jihar Bauci Bala Mohammed da ya ce kulorakwin/chloroquine na maganin cutar, shugaban kasar Madagaska ma ya ce ya gano maganin, haka nan Donald Trump na Amurka ya ce sun gano maganin ana nan za a soma gwajinsa da sauransu.

9. Yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya na korafin yau daya ga watan Mayu, ba dilin-dilin babu dalilinsa duk da Baba Buhari ya ba da umarni tun 23 ga watan jiya a hanzarta biya. Su kuwa malaman jami’a sun shiga wata na hudu ke nan ba dilin-dilin.

10. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da cutar kwaronabairos su 214 a kasar nan. Ga jihohin da abin ya shafa:

Kano 80
Legas 45
Gwambe 12
Bauci 9
Sakkwato 9
Barno 7
Edo 7
Ribas 6
Ogun 6
Abuja 4
Akwa Ibom 4
Bayelsa 4
Kaduna 3
Oyo 2
Delta 2
Nasarawa 2
Ondo 1
Kabbi 1

Sai jimillar da ke a jihohin da abin ya shafa:

Legas 979
Kano 219
Abuja 178
Gwambe 76
Barno 66
Ogun 56
Edo 44
Katsina 40
Bauci 38
Sakkwato 36
Kaduna 35
Oshun 34
Oyo 23
Akwai Ibom 16
Ribas 13
Kwara 11
Ondo 9
Delta 9
Ekiti 8
Taraba 8
Jigawa 7
Bayelsa 5
Zamfara 4
Inugu 3
Nasarawa 3
Neja 2
Abiya 2
Adamawa 2
Kabbi 2
Ebonyi 2
Binuwai 1
Anambra 1
Filato 1
Imo 1
Yobe 1

Gabadaya mutun 1932 ya harbu, 319 suka warke, 58 suka riga mu gidan gaskiya, 1555 ke jinya.

Idan na yi kuskure a jihohin ko hada hancin alkaluman a gafarce ni. Dan Adam nake.

Mu yi sahur lafiya, juma’a lafiya, buda baki lafiya.

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe don duba dandalina da ke dauke da labarun da na kawo muku daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis a dandalina na soshiyal midiya. Haka nan kamfanin sadarwa na DCL wato Dutsen Kura Communication Limited na Zahradeen Umar ya ware wa labarun nawa na kullum wani sashe na musamman da za a iya karanta labarun nawa da wasu karin bayani a kan abubuwan da nake yi. Za a iya lalubar kamfanin ta Intanet, a http://dclmedia24.com/2020/04/30/taskar-guibi-30-04-2020/ sai jaridar Kainuwa ta su Ibrahim Ammani da ke sanya labarun nawa a matsayin sharhin jaridar na kullum, sai su Umar Ridwan da a kullum suke sa labarun a dandalin wasaf na Matasa A Yau, sai su Bello Falama, da su Hajiya Hindatu Yawuri da ke yi wa rubutun labarun nawa hidima ba kadan ba. Akwai su da yawan gaske har da gidajen rediyo irin su Sifaida ‘yaf’yam duk ina godiya tare da dinbin masu bibiyata.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply