Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 01.11.2020

Taskar Guibi: 01.11.2020

344
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha biyar ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 162 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Gwambe 54
Abuja 35
Legas 26
Ogun 12
Filato 10
Kaduna 4
Ekiti 3
Edo 2
Oshun 2
Bayelsa 1
Imo 1
Ondo 1
Oyo 1

Jimillar da suka harbu 62,853
Jimillar da suka warke 58,675
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,144
Idan aka cire wadanda suka warke, da wadanda suka riga mu gidan gaskiya duk daga wadanda suka harbu za a samu jimillar da ke jinya.

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Kasashen Turai a kan a zabi Okonja Iweala a zaben ranar 9 ga watan nan na shugabanci hukumar hada-hadar kasuwanci ta duniya WTO.

3. Man fetur ya soma wahala a nan cikin garin Kaduna, haka na ji wani mai sayar da siminti na cewa yanzun buhu siminti naira dubu uku ne. Duk ana danganta wannan da wasoson kaya, da kona motoci da wasu suka yi lokacin zanga-zanga. Shi ya sa masu dakon man ta tankar mai suka dan janye daga debo man don tsaron dukiya.

4. Dakarun Amurka sun ceto wani Ba Amurke da aka yi garkuwa da shi a kasar nan.

5. Mutanen da suka kada kuri’a a zaben Amurka zuwa jiya da daddare, sun haura mutum miliyan tamanin da biyar.

6. Fitaccen afton nan na fim din James Bond, Sean Connery ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru casa’in a duniya.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilmi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin yau daya ga watan Nuwamba, an biya sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya albashi su ba a biya su ba. Ga korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da shi ma suke korafin an biya dukkan ma’aikata na gwamnatin tarayya, su har yau shiru.

8. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af!
Hmmmm!
A bi ni bashi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply