Home Sabon Labari Taskar Guibi 02.02.2020

Taskar Guibi 02.02.2020

78
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, bakwai ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyu ga watan Fabrairu na 2020.

1. Gwamnatin tarayya za ta kafa kwamitin da zai duba sharudda da dalilan da suka sa Amurka ta sa Nijeriya cikin kasashen da take kokarin hana su takardar izinin shiga kasarta wato VISA, saboda batutuwa na tsaro da tsoro da Amurka ke dubawa.

2. Ministan sadarwa Pantami, ya ce da aka aiwatar da tsarin nan na IPPIS a ma’aikatarsa, an samu ma’aikatan bogi su dubu sittin.

3. An tsinci gawar mutum daya da ya yi saura daga hudu da aka yi kidinafin a Kaduna, bayan ukun sun dawo gida.

4. Mutum daya ya mutu a yankin Kajuru da ke jihar Kaduna, sakamakon cutar lasa da ke da nasaba da bera, sai wani mutum guda ya harbu da cutar.

5. Al’umar Tyo-Mu da ke jihar Binuwai sun yi fada.

6. A jihar Taraba kidinafas sun yi kidinafin mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa NBA reshen jihar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya sai ga wata wai ita UWAR SHAGALI ta turo mun FRIEND REQUEST wato son ta yi abota da ni. Ga ta budurwa da dan kwali da riga da ke nuna tana neman abokin shagali. Sai na leka shafinta ko dandalinta na fesbuk tukuna don ba mamaki in ga kadan daga cikin hajarta da kuma abokanta da kawayenta. Ina ko lekawa sai na ga tana tallar magani ga wanda yake da lalurar gamsar da iyali. Na kuma dubawa sai na ga wata sanarwar da ke cewa ina namijin da ke son harka da mata ko koyon harka da mata, ko macen da ke son harka ko koyon harka da maza, to ga lambar waya nan sai mutum ya bi lambobin ta wasaf wato whatsAp. Har da karin bayanin za a tura wa namiji mace ko mata na harka duk inda yake so. Ita ma mace za a tura mata namiji ko maza na harka a duk inda take kuma take so. Sai na bibiyi lambobin, sai daya ta ce mun sai na tura katin naira dubu daya sannan in samu damar shiga sabgar. Daya lambar kuma ta ce sai na tura katin naira dari uku kafin a sa ni cikin wannan shagali. Tun daga nan sai na jiyo da baya, da ma ban yi ACCEPTING dinta ba. Sai na rubuta mata ta message wato ta bayan gida/fage, “Na ga hajarki, amma sai dai a sa ni kyauta” Sai ta ce “Wane ne ma ya turo maka FRIEND REQUEST?” Na ce ta duba da kyau ita ta turo mun. Can sai na ga ta dode hanyar da muke tattaunawar da ita wato ta yi BLOCKING.
Anya ba maza katti ke bude fesbuk da sunan mata suna sa mata na tura musu tsiraicinsu suna yadawa wadanda ke cikin irin wannan kungiya ko rukuni da aka fi sani da GROUP ba?
Sai a yi hattara don ina kyautata zatton maza ne zalla katti gardawa ke wannan sabga da sunan mata. Don har kidinafin za a iya ta wannan hanya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply