Home Taskar Guibi Taskar Guibi 02.05.2020

Taskar Guibi 02.05.2020

133
3

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, tara ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Mayu na 2020.

1. Jiya ta kasance daya ga watan Mayu, ranar ma’aikata a duniya bakidaya, inda ma’aikata a Nijeriya suka bi sahun na duniya wajen gudanar da bikin, sai dai ba cikin armashi ba wato LOW KEY, saboda yanayin cutar kwaronabairos da ake ciki, ga tsoron kada a rage ma’aikata daga aiki sakamakon durkusher tattalin arziki saboda cutar, wasu watansu na hudu ke nan ba albashi, wasu wata na biyu shiru, wasu gwamnoninsu sun yanke musu albashin da sunan gudunmawarsu ga cutar kwaronabairos, wasu fiye da shekara daya suna jiran ariyas. Da dai sauran dinbin matsaloli da ma’aikaci ke ta dambe da su a Nijeriya. Inda shugaban kungiyar kwadago na kasa Ayuba ya yi gargadin ba za su yarda da kwashe albashin ma’aikata ko kokarin raba su da aikin saboda kwaronabairos ba. Shi kuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari jinjina wa ma’aikata ya yi saboda jajircewarsu a wannan yanayi da aka shiga, tare da ba su tabbacin ba za a sallami wani ma’aikaci ba.

 

2. Wata na hudu ke nan ba a biya malaman jami’o’i albashi ba, su kuma ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya da suka amince suka shiga tsarin IPPIS, sun yi korafin haka nan suka yi bikin ranar ma’aikata ta bana babu albashi, duk da shugaban kasa ya ce a hanzarta biya tun ranar 23 ga watan jiya. Da ma kuma suna korafin sun haura shekara daya suna jiran ariyas, ba amo ba labari.

 

3. Kwamitin shugaban kasa na kula da yakar cutar kwaronabairos na karfafa gwiwar a samar da maganin cutar kwaronabairos a nan gida Nijeriya, ba sai an jira magani daga kasashen waje ba. Har hukumar lafiya ta duniya ta karfafa wa Njjeriya gwiwar ta samo maganin cutar, kamar yadda a yanzun a duniya akwai magunguna tamanin da tara da aka gano na cutar, ana nan an soma gwada guda bakwai a gani. A yanzun a duniya mutum miliyan daya ya warke daga cutar, dubu dari uku da talatin da uku suka riga mu gidan gaskiya, kuma zuwa yanzun mutum miliyan uku da ‘yan kai suka harbu a duniya. A cire miliyan daya da ya warke, da kuma wadanda suka rasu.

 

4. Hukumar agajin gaugawa ta kasa NEMA ta ce za ta soma kai motocin daukar kaya dankare da kayan abinci Kano don tallafa wa mutanen Kano.

 

5. Shugaba Trump na Anurka ya ce in duk jikinsa kunnuwa ne, babu wanda zai iya gamsar da shi cewa ba kasar Sin/Caina ba ce ta kirkiro da cutar kwaronabairos. Saboda haka ya ce a binciki Caina da kyau.

 

6. Sojojin Nijeriya sun ce sun kashe wasu ‘yan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa.

 

7. Shugaban kungiyar kwadago ya nemi gwamnatin tarayya ta kara rage farashin mai tunda ya kara yin arha a kasuwar duniya.

 

8. Yau asabar, al’umar jihar Kaduna za ta sake shakar iskar ‘yanci daga kullen da aka tilasta mata don rigakafin yaduwar cutar kwaronabairos. Za a fita daga karfe takwas na safe, a koma karfe shida na yamma sannan an ware kasuwanni na unguwa a makarantun firamare mafi kusa, da jama’a za su iya zuwa sayayyar kayan abinci ba sai an yi tattaki zuwa kasuwanni da ke nesa ba. Da ma gwamnatin jihar Kaduna ta ware laraba da asabar don a dinga fita daga kulle.

 

9. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci akwai sabbi da suka harbu da kwaronabairos a kasar nan su 230 kamar haka:

Kano 92
Abuja 36
Legas 30
Gwambe 16
Bauci 10
Delta 8
Oyo 6
Zamfara 5
Sakkwato 5
Ondo 4
Nasarawa 4
Kwara 3
Edo 3
Ekiti 3
Barno 3
Yobe 3
Adamawa 2
Neja 1
Imo 1
Ebonyi 1
Ribas 1
Inugu 1

A yanzun jimillar wadanda suka harbu 2170, 351 sun warke, 68 sun rasu, 1851 suna jinya.

Ga adadin wadanda suka harbu a jihohin da abin ya shafa:

Legas 1006
Kano 311
Abuja 214
Gwambe 92
Barno 69
Ogun 56
Bauci 48
Efo 47
Sakkwato 41
Katsina 40
Kaduna 35
Oshun 34
Oyo 29
Delta 17
Akwa Ibom 16
Kwara 14
Ribas 14
Ondo 13
Ekiti 11
Zamfara 9
Taraba 8
Jigawa 7
Nasarawa 7
Bayelsa 5
Inugu 4
Adamawa 4
Yobe 4
Neja 3
Ebonyi 3
Abiya 2
Imo 2
Kabbi 2
Binuwai 1
Anambra 1
Filato 1

In an hada ya zama 2170, a cikinsu ne 351 suka warke, 68 suka riga mu gidan gaskiya, sai saura 1851 da ke jinya.

Kamar kullum idan na yi kuskure ko a kason jihohin ko hada hancin alkaluman a gafarce ni. Dilin-dilin af kai ashe ba shi ba ne! Ku banki kun cika zolaya a irin wannan lokaci na zaman dakon abubuwa.

Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.

Af! Za a iya lekawa TASKAR GUIBI da ke jaridar DCL Hausa a:
http://dclmedia24.com/2020/05/02/taskar-guibi-02-05-2020/

Don samun wadannan labaru da dumi-duminsu.

Sai jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da ta fito jiya da safe, don duba wadannan labarun da na wallafa a dandalina na soshiyal midiya na mako guda.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

3 COMMENTS

Leave a Reply