Home Labarai Taskar Guibi: 02.07.2020

Taskar Guibi: 02.07.2020

308
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da aahirin.

1. Ga ma’aikatan bangaren ilimi na gwamnatin tarayya har yau watan Yuni bai mutu ba, ballantana a shiga Yuli. Watau yau talatin da biyu ga watan Yuni, ba biyu ga watan Yuli ba, saboda ba dilin-dilin babu labarinsa.

2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wajen wata uku ke nan, suna dakon ariyas na sabon albashi.

3. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairu na shekarar nan.

4. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman Majalisar Zartaswa na jiya laraba.

5. ‘Yan Majalisar Dokoki ta Kasa sun ji haushin abin da karamin ministan kwadago Kiyamo ya musu, na yin sa-in-sa da su, sun ce sun dakatar da shirin daukar aikin na mutum dubu dari bakwai da saba’in da hudu, tare da bukatarsa ya gurfana a gaban majalisar.

6. An kwaso ‘yan Nijeriya su dari bakwai da saba’in da biyu daga Kenya da Uganda.

7. Gwamnatin Tarayya ta amince jiragen sama za su dawo da zirga-zirga ta cikin gida daga laraba mai zuwa, takwas ga watan nan, a tasoshin jiragen sama da ke Abuja da Legas, sai ranar goma sha daya ga watan nan na Kano da Fatakwal da Owerri da Maiduguri su biyo baya, sauran tashoshin kuma daga ranar goma sha biyar ga watan nan.

8. Shugaban Kasa ya tura wa Majalisar Dattawa sunayen mutum arba’in da biyu da yake so ta amince masa ya nada su jakadun kasar nan.

9. Tukur Buratai ya hori sojoji su dinga bin ‘yan bindiga har inda suke suna maganinsu.

10. Kotu ta ki amincewa da bukatar wanda ake zargin rikakken kidinafa ne, Hamisu Wadume ta a ba da belinsa, a shari’ar da ake masa shi da wasu mutum shida. Kotu ta ce tunda ana shari’ar babu bata lokaci, babu dalilin ba da belinsu.

11. Majalisar Dokoki ta Kasa ta soma bincikar Babban Akanta na Kasa.

12. Wasu bayanai na nuna gwamnatin tarayya ta kara kudin man fetur, naira dari da arba’in kowacce lita a yanzun.

13. ‘Yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare wasu kauyukan jihar Katsina, sai ‘yan kungiyar Boko Haram da suka nemi gwamnatin tarayya ta ba su wasu daruruwan miliyoyin naira don sako wasu da suke tsare da su, ko su kashe su, kamar yadda suka saba.

14. Gwamnan jihar Delta Ifeanyi da matarsa, sun harbu da kwaronabairos, da ya zama shi ne gwamna na shida da ya harbu.

15. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari bakwai da casa’in a jihohi da alkaluma kamar haka:

Delta 166
Legas 120
Inugu 66
Abuja 65
Edo 60
Ogun 43
Kano 41
Kaduna 39
Ribas 32
Bayelsa 29
Katsina 21
Imo 20
Kwara 18
Oyo 11
Abiya 10
Binuwai 6
Gwambe 4
Yobe 2
Bauci 2
Kabbi 2

Jimillar wadanda suka harbu, mutum dubu ashirin da shida, da dari hudu da tamanin da hudu. Wadanda suka warke, mutum dubu goma da guda dari da hamsin da biyu. Wadanda suka riga mu gidan gaskiya mutum dari shida da guda uku. Wadanda ke jinya mutum dubu goma sha biyar, da dari bakwai da ashirin da tara.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wadanda ke da ababen hawansu ke zirga-zirga a cikin garin Kaduna, akwai kotunan-tafi-da-gidanka a wurare daban-daban. Idan an kama ka, ba ka sa takunkumi ba, tarar naira dubu biyar. In ku biyu ne a motar, tarar dubu goma, in ku uku ne tarar dubu goma sha biyar. Sai dai akwai wanda na ji yana korafin wani jami’i ya kama su, su uku a cikin motarsa ba su sa takunkumi ba, ya shiga motarsu, ya kira ‘yan sanda a waya cewa mai motar ya yi ABDUCTING dinsa. Kamar yadda mai motar ya yi bayani. Aka kama mai mota sai kotun tafi-da-gidanka da ke zama kusa da ofishin ‘yan sanda da ke Unguwar Sanusi. Mai shari’a ya ci shi tarar naira dubu arba’in ta laifin ABDUCTION, sai tarar naira dubu goma sha biyar ta kin sa takunkumi da yake su uku ne a motar. Akwai takunkumin a motar amma ba su sanya ba. Mai shari’a ya musu sassaucin tarar takunkumi ya ce su biya naira dubu biyar maimakon naira dubu goma sha biyar, kamar yadda mai motar ya yi zargi. Nan take suka biya naira dubu arba’in da biyar, tarar takunkumi da ta ABDUCTION. Don an ba su zabin ko su biya, ko a kai su gidan gyara halinka su yi aikin ci gaban al’uma na tsawon wata uku. Sai dai na ji wani lauya na ba su shawarar su rubuta takardar koken abin da aka musu, su kai wa babbar mai shari’a ta jihar Kaduna.
Tambayata a nan, a kundin tsarin mulkin kasar nan akwai dokar da ta yarda wani jami’i don ya kama ka, ko yana tuhumarka ya bude maka kofar mota, ya shiga ya zauna ya hakimce? Ina lauyoyin suke irin su Barista El-Zubair ku duba mana.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply