Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 03.01.2021

Taskar Guibi: 03.01.2021

377
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, goma sha tara ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fitayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Janairu, na shekerar 2021.

1. Gwamnatin Tarayya ta dage hanin da ta yi na zuwa sauya wa mutum layinsa na waya SIM, da ya bace, ko aka sace, ko ya lalace. Da ke nufin idan an sace maka layinka ko wani abu ya same shi za ka iya zuwa ka yi WELCOME BACK wanda aka dan dakatar da farkon wannan rajistar ta dan kasa da hade lambar da layin waya.

2. Sojojin sama sun kaddamar da rawar soja da suka kira TAIMAKO YA ZO a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin kidinafas da makasa da sauran masu aikata miyagun laifuka a hanyar.

3. Shi kuwa Dafta Gumi, shahada ya yi ya kutsa rugagen kidinafas da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja domin nuna musu Allah, da kawar musu da jahilcin addini, domin su daina kidinafin. Saboda ya yi imanin bindiga kadai ba za ta magance kidinafin da fulanin rugagen hanyar Kaduna zuwa Abuja ke yi ba.

4. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe wani malami da wasu mutum biyu. Haka nan a yankin Kajuru sun kashe wani jagoran al’uma bayan sun yi kidinafin dinsa. A Godogodo ma sun kashe wani sarkin yaki.

5. ‘Yan sanda sun dakile wani kidinafin da aka so yi a Shinkafi tare da ceto mutun guda.

6. Mutanen Madaka ta jihar Neja na neman a agaza musu bangaren tsaro, haka nan a karamar hukumar Rafi, masarautar Kagara, ana ci gaba da kashe masu gari da talakawa. Sannan makasa sun kashe wasu manona bakwai da suka je gona girbe amfanin gonakinsu a Mashegu duk da ke jihar Neja. Sun nemi sai manoman sun biya su kudi kafin su barsu su yi girbin. Suka ki suka tafi da ‘yan sintiri domin ba su kariya. Makasan suka same su suka kashe manoman bakwai a gona.

7. Gwamnan jihar Barno Zulum, ya nemi NEMA wato hukumar kula da agajin gaugawa ta kasa, ta agaza wa ‘yan gudun hijira na jihar su dubu dari takwas.

8. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 576 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 277
Abuja 90
Oyo 51
Nasarawa 49
Bauci 11
Imo 11
Kano 11
Edo 11
Filato 11
Ogun 9
Oshun 5
Jigawa 3
Ribas 2

Jimillar da suka harbu 89,163
Jimillar da suka warke 74,789
Jimillar da ke jinya 13,079
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,302

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, da ya je ya cika musu alkawarin gyaran gada, da ya musu alkawari lokacin yakin neman zabe. Ga shi yana shirin sauka bai je ya gyara musu ba.

10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan citta za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Mu ci gaba da addu’a Allah Ya mana maganin kidinafas da makasa Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply