Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 04.07.2020

Taskar Guibi: 04.07.2020

263
0

Assalamu alaikum barkanmu da asabar, kuma yanzun karfu uku na dare da wasu mintoci ana ta ruwan sama, sai dai tasowar hadarin suka dauke wuta, kuma da ma rabonmu da wutar tun shekaranjiya, sai cikin daren nan suka dawowa da ita, goma sha biyu ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Yuli, shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Bayanin da nake samu shi ne watan Yuni ya mutu, har Juli ya kama yau hudu ga wata saboda ana ta gani ko jin dilin-dilin.

2. Hukumomin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince cewa REMDISIVIR na maganin kwaronabairos.

3. Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa NAFDAC, ta ce zuwa yanzun masu magungunan gargajiya su ashirin suka mika mata magungunansu don gwadawa a matsayin maganin kwaronabairos.

4. Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta Kasa ta yi wa manyan ‘yan sanda su dubu shida, da dari shida da goma sha takwas karin girma, da sauya wa wasunsu wuraren aiki.

5. Sojojin sama sun ce sun kai farmaki mabuya daban-daban ta kungiyar Boko Haram da ke Mainyakare a jihar Barno, inda suka kashe mayakan da lalata muhallansu da kayan aikinsu.

6. Kaf din kungiyoyin fulani makiyaya da ke kudancin jihar Kaduna, sun yi kiran a yi cikakkiyar biyan wadanda rikici ya ritsa da su a karamar hukumar Zangon Kataf, da ta Kauru kwanan nan,, tare da yin kira ga wadanda suka tsira daga hare-haren da aka kai musu, su yi hakuri su zauna lafiya, da ci gaba da rungumar kaddarar da ke yawan auka musu a zamansu da abokan zama.

7. A shekaranjiya APC ta nada Ganduje don jagorantar ganin APC ce ta lashe zaben gwamnan jihar Edo, to PDP ta nada Wike a jiya a matsayin nata jagoran. Ga Wike PDP ga Ganduje APC za a kara ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.

8. An debo ‘yan Nijeriya su tamanin da shida daga kasar Sudan.

9. Gwamnan jihar Bauci Bala Muhammad ya dakatar da Sarkin Misau Alhaji Ahmad Suleman saboda wani rikici da ya auku a Hardawa har aka kashe mutum tara, aka ji wa da dama rauni.

10. A duniya a yanzun mutum kusan miliyan goma sha daya ya harbu da kwaronabairos.

11. Shugaban ma’aikatan fadar Lalong ya harbu da kwaronabairos.

12. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari hudu da hamsin da hudu, a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 87
Edo 63
Abuja 60
Ondo 41
Binuwai 32
Abiya 31
Ogun 29
Oyo 19
Kaduna 17
Delta 16
Inugu 15
Barno 14
Filato 9
Nasarawa 8
Kano 5
Bauci 4
Gwambe 2
Katsina 1
Kogi 1

Jimillar wadanda suka harbu, mutum dubu ashiriin da bakwai, da dari biyar da sittin da hudu. Wadanda suka warke, dubu goma sha daya da sittin da tara, wadanda suka riga mu gidan gaskiya, mutum dari shida, da ashirin da takwas, sai wadanda ke jinya su dubu goma sha biyar, da dari takwas da sittin da bakwai.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Har sun kara kudin mai don jiya na taso aiki da almuru, na biya gidan man Royal kafin ka karasa randar labintis, ta babbar kasuwa in ka fito Nefa, in sha man, sai na tarar naira dari da arba’in da uku kiwacce lita. An ce wasu gidajen man kowacce lita naira dari da arba’in da biyar ce, ga shi da ka sha man kamar ya bi iska, ga tauye mudun ma’aunin man, kana ganin ka sha man dubu daya, a zahiri na naira dari takwas aka dura maka. Kaico! Talakan Nijeriya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply