Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 05.05.2020

Taskar Guibi: 05.05.2020

305
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha biyu ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Mayu na shekarar 2020.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin an mike tsaye don tarbe yaduwar cutar kwaronabairos.

2. Ministan Labaru Lai Mohammed ya bukaci bankuna su dinga makare rumbunansu na kudi ATM da kudi sosai saboda kauce wa cincirindon da mutane ke yi a ATM na banki guda daya tal don cire kudi musamman ranakun da aka sassauta kulle.

3. Gwamnatin Tarayya ta ce daga gobe laraba za a fara kwaso ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje zuwa gida Nijeriya, inda a ranar goma ga watan nan ake sa ran soma kwaso ‘yan Nijeriya da ke Amurka su fiye da dari bakwai.

4. An samu an karbo dala miliyan dari uku daga Amurka da Jersey, kudaden da ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Abacha ya kai su can. An ce sai da Amurka ta figi nata rabon a matsayin tukwici. Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi amfani da kudin wajen kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kano da sauran hanyoyin da ake kan yi.

5. Kotu ta ba da belin tsohon ministan ayyuka na musamman Kabiru Turaki da hukumar EFCC ta gurfanar da shi gaban kotu jiya, tana zarginsa ya dafe wasu makudan kudi da shi da wasu.

6. Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu, JAMB ta mayar wa gwamnatin tarayya naira biliyan bakwai ta jarabawar da aka yi bana.

7. Dangote ya ba da gudunmawar na’urar da za a iya gwajin mutum dari hudu a rana, nan da kwanaki kadan masu zuwa har mutum dubu daya za a iya gwadawa a rana don gano wanda ya harbu da cutar kwaronabairos a jihar Kano. Haka nan gidauniyar BUA ita ma ta ba da tata gudunmawar ga yaki da cutar a jihar Kano.

8. Hukumar Kididdiga Ta Kasa ta ce jihar Sakkwato ce ta fi yawan matalauta a kasar nan.

9. Gwamnatin jihar Binuwai ta tarbe wata babbar mota dauke da almajirai goma.

10. An sanar da rasuwar wani babban mataimakin kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano.

11. Gwamnatin jihar Legas ta ce ba ta gamsu da yadda jama’a ke kiyayewa da dokokin walwala da aka gindaya mata bayan sassauta kullen da aka yi a jihar ba.

12. Amurka da Caina na ci gaba da zargin junansa a kan cikinsu wani ne ya kirkiro da cutar kwaronabairos da gangan.

13. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce babu mamaki Amurkawa su dubu dari za su riga mu gidan gaskiya sakamakon kwaronabairos.

14. Shugabannin kasashen Turai sun dau alkawarin ba da naira biliyan sittin da biyar da rabi don samar da maganin kwaronabairos.

15. Ma’aikatan kwalejojin ilimi da na foliteknik na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin har yau ba dilin-dilin babu dalilinsa na watan jiya, duk da tun 23 ga watan jiya Baba Buhari ya ce a hanzarta biya saboda yanayin da ake ciki. Su ma malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya wata na hudu ke nan babu dilin-dilin duk da Baba Buhari ya ce a hanzarta a biyu su tun 23 ga watan jiya.

16. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci akwai sabbi da suka harbu da cutar kwaronabairos su 245 a jihohi kamar haka:

Legas 76
Katsina 37
Jigawa 32
Kano 23
Abuja 19
Barno 18
Edo 10
Bauci 9
Adamawa 6
Oyo 5
Ogun 5
Ekiti 1
Oshun 1
Binuwai 1
Neja 1
Zamfara 1

Da ke nuna jimillar mutane 2802 suka harbu zuwa jiya da daddare. Daga ciki 417 sun warke, 93 sun riga mu gidan gaskiya, sai 2292 da ke jinya.

Ga yawan wadanda suka harbu a jihohin da abin ya shafa:

Legas 1183
Kano 385
Abuja 297
Barno 100
Gwambe 96
Ogun 85
Katsina 83
Kaduna 81
Bauci 80
Sakkwato 66
Edo 62
Oyo 39
Jigawa 39
Oshun 37
Delta 17
Akwa Ibom 16
Kwara 16
Ribas 14
Ondo 13
Zamfara 13
Yobe 13
Ekiti 12
Adamawa 12
Kabbi 12
Nasarawa 11
Taraba 8
Inugu 8
Bayelsa 5
Ebonyi 5
Neja 4
Filato 3
Abiya 2
Binuwai 2
Imo 2
Anambra 2

Jimilla 2802, 417 sun warke, 93 sun riga mu gidan gaskiya, 2292 ke jinya.

Mu yi sahur lafiya, mu yuni lafiya, mu wayi gari lafiya.

Af! Akwai korafe-korafe jiya cewa ‘yan sandan da aka girke jiya a mahadar titin Foliteknik da titin Faki rod da ke Tudun Wada/Sabon Garin Kaduna na cin zarafin musu ababen hawa, ciki har da wadanda aikinsu na musamman ne kuma sun nuna katin shaida. Da na ji korafin ni ma na je kuma wani dan sanda ya ci zarafina duk da na nuna katin shaida. Na kuma dauka a waya. Saboda haka hukumomin ‘yan sanda na unguwar Sanusi su sanya ido kafin batun ya kai ga HUMAN RIGHT COMMISSION don abin da suke nema ke nan ido rufe.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply