Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 05.06.2020

Taskar Guibi: 05.06.2020

126
0

1. Kwamitin Shugaban Kasa a kan kwaronabairos ya amince kamar yadda hukumar lafiya ta amince a ci gaba da gwajin kulorakwin wajen magance kwaronabairos.

2. Majalisar Wakilai ta ki amincewa da bukatar a dinga dandake duk wanda aka samu ya yi wa wata fyade.

3. Kungiyar Dalibai ta Kasa ta roki Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin fyade.

4. Kungiyoyin kare hakkin bil’Adama daban-daban na ta korafi a kan yadda aka ware naira biliyan daya da rabi da ‘yan kai domin gyara titin saukar jiragen sama a tasha daya, kuma ga bilyan biyu da rabi da ‘yan kai na gyaran ginin majalisar dokoki ta kasa duk ba a zaftare kudin a sabon kasafin da aka yi ba, sai kasafin lafiya da na ilimi matakin farko aka wawuke. Suka yi korafin gyaran titin jirgin sama da na ginin majalisa ya fi lafiyar talaka da karatun ‘ya’yansa ke nan!

5 Wasu rahotanni na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutum saba’in a jihar Zamfara.

6. A jihar Kogi wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe ‘yan sanda kusan takwas.

7. Sojoji sun ce suna nan suna yakar ‘yan bindiga da kidinafas na jihohin Zamfara, da Sakkwato, da Nasarawa, da Kabbi, da Kaduna, da Katsina, da Neja, da Kogi, da Filato zuwa Binuwai da sauransu.

8. Gwamnan jihar Katsina Masari ya bukaci dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi kowa ya koma aiki ranar litinin mai zuwa, kulle ya kare daga ranar.

9. Gwamnan jihar Legas ya ce daga 19 ga watan nan, dokar hana sallah da zuwa coci ta kare daga ranar.

10. Gwamnatin jihar Kwara ta ce a soma zuwa Sallar juma’a daga yau, jibi lahadi kuma a je coci dokar hana sallah da coci ta kare daga jiya.

11. An sallami almajirai da aka mayar wa jihar Jigawa abinta su duba daya da dari uku da talatin da uku daga inda ta killace su, aka sallani kowanne zuwa gidan iyayensa, aka ba kowanne naira dubu goma da tufafi, ashirin da uku daga cikinsu da aka gano sun harbu da kwaronabairos an ci gaba da jinyarsu.

12. A jihar Kano za a bi gida-gida ana gwajin kwaronabairos.

13. Gwamnan jihar Kaduna ya ce a makon gobe za a ji halin da ake ciki a game da dokar kulle da hana jam’i ko zuwa coci.

14. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya, da kusan wata biyu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi. Har yau shiru. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

15. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito da safiyar nan don karanta labarun da na bayar daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis a dandalina na jaridar. Haka nan akwai jaridar Muryar ‘Yanci ta rediyo da talabijin na Liberty da ke buga labarun nawa a kullum, haka nan dandalin Kainuwa, da dandalin Matasa A Yau, da sauran dandali, da gidajen rediyo da talabijin da ke watsa labarun da nake rubutawa kullum. Duk ina godiya.

16. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 350, a jihohi da alkaluman kamar haka:

Legas 102
Ogun 34
Abuja 29
Barno 26
Kaduna 23
Ribas 21
Kwara 16
Ebonyi 17
Katsina 14
Edo 10
Delta 10
Kano 10
Bauci 10
Bayelsa 9
Imo 8
Filato 4
Ondo 3
Nasarawa 2
Gwambe 1
Oyo 1
Kogi 0
Kuros Ribas 0

Da ke nuna zuwa jiyan da daddare kowacce jiha tana da kaso kamar haka:

Legas 5,542
Kano 980
Abuja 792
Katsina 385
Edo 351
Barno 322
Kaduna 320
Oyo 318
Ogun 316
Ribas 290
Jigawa 274
Bauci 256
Gwambe 170
Kwara 127
Delta 116
Sakkwato 115
Filato 113
Nasarawa 90
Ebonyi 80
Zamfara 76
Yobe 52
Imo 47
Oshun 47
Akwa Ibom 45
Adamawa 42
Neja 41
Ondo 36
Kabbi 33
Bayelsa 30
Ekiti 25
Inugu 24
Taraba 18
Abiya 15
Binuwai 13
Anambra 12
Kogi 3
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 11,516
Jimillar wadanda suka warke 3,535
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 323
Jimillar wadanda ke jinya 7,658

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya wani tsohon maigidana Abdullahi Otijele ya yi tsokaci a rubutana na jiya kanar haka:

“Mal. Guibi na gasheka, amma ka manta da woni buba labari wanda ya mamaye Yana gizo a kwana biyu Nan cewa buba cotu tarewa (federal court) ya marma masaurotar Igala watau Igala kingdom yakin Lokoja, Ajaokuta da Koton Karfi. Bayan Mai girma, Attah Igala ya nuna hujojin shi saiwa Igala ce Ike da wuraren.
Bajaka Taya mu murka ba?”

Malan Abdullahi ina taya ku da sauran al’umar Igala murna. Abin da wasu ba su sani ba, a jihar Kogi na auri Igala Harira, da Igbira Hauwa, da Basange Aisha.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply